Hukumar ‘yan sandan Najeriya, ta kaddamar da shirin tantance jami’an ta domin ciyar dasu gaba, har ila yau dai shirin tantancewar zai zakulo jami’an ‘yan sanda da suka yi fice ta hanyar karo karatu mai shaidar digiri ko kuma difloma.
Kwamishina ‘yan sanda na jihar Bauchi, Muhammad K. Muhammad, yace “jihohin Najeriya, baki daya ko ina aka bada izinin ayi wannan tantancewar na farko mu tabbatar cewa kayi karatun na biyu kuma mu tabbatar cewa kana da izinin yin wannan karatun mu tabbatar cewa bana wani ne bane kuma ba hanya na rashin gaskiya kabi ba ka samu wannan takardan.”
Wasu daga cikin jami’an ‘yan sandan da suka halarci wurin tantance sun nuna farin cikinsu da wannan damar da hukumomin ‘yan sandan suka basu domin nuna takardunsu na Karin ilimi da niyyar ciyar dasu gaba.