Sudan Ta Ce ta Kwato Wata Tungar 'Yan Tawaye

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan

Jami’an Sudan sun ce sojojin gwamnati sun fatattaki ‘yan tawaye daga garin Kurmuk dake kusa da bakin iyakarsu da Sudan ta Kudu

Rundunar sojojin Sudan ta ce ta kwato wata tungar ‘yan tawaye a Jihar An Nīl al Āzraq ko Blue Nile dake bakin iyakarta da Sudan ta Kudu.

Jami’an Sudan sun fada jiya alhamis cewa sojojin gwamnati sun samu nasarar fatattakar ‘yan tawaye daga garin Kurmuk dake kusa da bakin iyakar. Suka ce sun kwace dukkan garin daga hannun sojoji masu nuna biyayya ga kasar Sudan ta Kudu.

A bayan Jihar ta An Nīl al Āzraq, sojojin gwamnatin Sudan su na fafatawa da ‘yan tawaye a wasu jihohin bakin iyaka guda biyu, Kordofan ta Kudu da Abyei, dukkansu masu arzikin man fetur a bakin iyakar kasashen biyu.

Har yanzu Sudan da Sudan ta Kudu ba su warware batun yadda zasu raba kudaden shiga na mai da kuma shata iyakarsu ba a bayan da Kudu ta balle. Sudan ta Kudu ta mallaki akasarin man, amma kuma tana bukatar tasoshin lodin mai na Sudan dake gabar bahar maliya domin kai shi kasuwa a kasashen waje.