Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar EU tace Malawi ta kama shugaban Sudan

Shugaban Sudan Omar Al Bashar daga hannun dama.
Shugaban Sudan Omar Al Bashar daga hannun dama.

Kungiyar kasashen turai, ta roki kasar Malawi data mutunta umarnin da kotun kasa da kasa ta bayar, ta kama shugaban kasar Sudan Umar Al Bashir a yayinda ziyarar daya kai kasar.

Kungiyar kasashen turai, ta roki kasar Malawi data mutunta umarnin da kotun kasa da kasa ta bayar, ta kama shugaban kasar Sudan Umar Al Bashir a yayinda ziyarar daya kai kasar.

Yau juma’a mai magana da yawur kungiyar Catherine Ashton tace, ta damu da wannan ziyarar da shugaba Bashir ya kai Malawi, a saboda haka tayi kira ga kasar Malawi data mutunta alkawuran data yi karkashin dokokin kasa da kasa.

Jiya Alhamis shugaba Umar Al Bashir ya kai ziyara kasar Malawi domin halartar taron kungiyar harkokin kasuwancin kasashen gabashin da kudancin Afrika.

Jiya Alhamis ne kuma, ma’aikatar harkokin wajen Malawi tace bata da niya ko kuma shirin kama Mr Bashir, tana mai fadin cewa yana da yancin yin abinda yaga dama, kuma shi bakon shugaba Bingu Wa Mutharika ne.

Babar jam’iyar masu hamaiyar kasar Malawi da wsasu kungiyoyin hankorion kare hakkin jama’a guda biyu suma suna matsawa gwamnatin Malawi lambar cewa ta kama shugaba Al Bashir ko kuma ta hana shi shiga kasar.

XS
SM
MD
LG