NIAMEY, NIGER - A dalilin haka ne kuma hukumomin suka umurci ‘yan sanda su tisa keyarsa bayan da gwamnatin Faransa ta yi watsi da matakin korarsa daga Nijar din, a ci gaba da takun sakar da ke tsakanin kasashen biyu sanadiyar juyin mulkin da aka yi wa zabeben Shugaban kasar na dimokradiya Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Sanarwar da ma’aikatar Ministan harakokin wajen Nijar ta aika wa ma’aikatar harakokin wajen Faransa da hantsin yau Alhamis 31 ga watan Agusta ta fara ne da cewa bakin alkalami ya rigai ya bushe game da matakin soke takardar huldar jakadanci da kasar ta ba shi.
Hakan na nufin bayan shudewar wa’adin sa'o'i 48 domin ya fice daga Nijar, jakadan ba zai sake samun damar morar dukkan abubuwan alfarma da rigar kariyar da ya ke da su a baya ba, a matsayinsa na daya daga cikin ma’aikatan ofishin jakadancin Faransa a Nijar.
Sanarwar ta kara da cewa an soke kati da bizar jakada Sylvain Itte da na iyalinsa sannan hukumomin sun umurci ‘yan sanda su tisa keyarsa daga Nijar.
Tsohon shugaban kungiyar sa ido kan ayukan watsa labarai wato ONIMED Jaharou Maman ya yi wa kasashen biyu hannunka mai sanda.
A yanzu haka wasu kungiyoyin fararen hula na ci gaba da kiraye-kirayen jama’a domin halartar zaman dirshan a kofar sansanin sojan Faransa da ke gab da filin jirgin sama na birnin Yamai a ranar Asabar 2 ga watan Satumba.
Wannan ne wuni na karshe na wa’adin da Majalissar CNSP ta bai wa Faransa don ficewar dakarunta daga Nijar a wani bangare na matakan tsinke yarjejeniyar ayyukan sojan da ke tsakanin kasashen biyu.
Hukumomin Faransa sun fada a yau Alhamis cewa suna bin matakan tsaro sau da kafa a ofishin jakadancin kasar da ke Yamai. Sun kuma jaddada cewa sojojin juyin mulki ba su da hurumin korar jakada Sylvain Itte saboda dalilai na rashin halacci inji su.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5