Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Juyin Mulki Nijar Sun Dorawa Kungiyoyin Agaji Nauyin Kula Da ‘Yan Ciranin Kasar


Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijar
Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijar

Matakin na zuwa ne sakamakon janye wasu ayyukan tallafawa 'yan cirani da kasashen suka yi bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.

AGADEZ, NIGER - Hukumomin da ke kula da ‘yan cirani da kasar Algéria ta koro sun bayyana damuwa bayan da kungiyoyin agaji suka dakatar da tallafin da suke bai wa hukumomin domin gudanar da daukar nauyinsu.

Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijar
Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijar

‘Yan ci rani da kasar Algeria ta koro da suka je kasar domin samun abin sakawa a bakin salati sun samu kansu a cikin tsaka mai wuya bayan da kungiyar tarayyar Turai ta dakatar da tallafin da take bai wa Nijar sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli.

Hakan na faruwa ne sakamakon yadda kasar Algeria ke ci gaba da koro ‘yan Nijar daga kasar.

A baya sai da kasar ta koro wasu yara ‘yan kasar Nijar akalla fiye da 60 da suka je kasar ta Algeria ci rani, abin da ake ganin zai dagula al’amurra na daukar nauyin ‘yan ciranin.

Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijar
Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijar

Isma’il Toufa Ibrahim wani jami’i a ma’aikatar da ke kula da kananan yara ya ce tuni dai sojojin da suka yi juyin mulkin suka kira kungiyoyin agaji da ke zaune a Nijar da su dauki nauyin ‘yan kasar Nijar.

A nasu bangare kungiyoyin agajin irin hukumar da ke kula da bakin haure cewa suka yi sun yi na’am da bukatar da hukumomin suka gabatar musu na daukar nauyin ‘yan ci ranin Nijar da kasar Algeria ta koro a cewar Mahaman wani jami’i a hukumar da ke kula da bakin haure.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Sojojin Juyin Mulki Nijar Sun Dorawa Kungiyoyin Agaji Nauyin Kula Da ‘Yan Ciranin Kasar. mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG