An samu ceto sojoji uku daga cikin 37 dake wannan jirgin ruwa mai suna “Le Mundemba”, wanda ya kife a jiya Lahadi da misalin karfe 6 na safe a kusa da gabar Debunsha.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta aikewa da manema labarai ta ce “har yanzu ba a tabbatar da musabbabin wannan hadari ba.”
Cikin gaggawa aka zuba ma’aikatan aikin ceto da bincike bayan da hanyar sadarwa ta katse tsakanin su da jirgin ruwan sojojin, har ya zuwa yau Litinin ana ci gaba da gudanar da binciken.
Kamaru dai ta karbi ikon yankin Bakassi mai albarkatun man fetur daga hannun Najeriya, shekaru uku da suka gabata a sakamakon wata yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ido wajen kullawa.
Mayar wa da kasar Kamaru wannan yanki ta kawo karshen shekara da shekarun da aka yi ana takaddama kan wake da mallakin wannan yanki.