Yankunan kasashen biyar da suka hada da Somalia da Ethiopia da Kenya da Tanzania da kuma Uganda, baki ‘daya sun sami karancin ruwan sama.
Matsalar fari da suka samu hade da wata tsutsa mai lalata kayayyakin amfanin gona, sun bar miliyoyin mutane a gabashin Afirka cikin karancin abinci.
Duk kuwa da yawan samun lalacewar kayan amfanin gona da aka samu, an sami asarar dabbobi wanda hakan ya haddasa karancin madara.
Cibiyar MDD ta ce ana kyautata tsammanin halin da gandun daji da dabbobin da ake kiwo ke ciki zai ci gaba da tabarbarewa har sai watan Oktoba, lokacin da damuna zata sake zuwa.
Facebook Forum