Wata kotu a birnin Yamai dake Jamhuriyar Nijar ta sallami wani mai gwagwarmaya bayan da ya shafe makwanni uku a tsare a gidan yari saboda zarginsa da aka yi da yi wa alkalai kazafin cin hanci ta hanyar shafin facebook.
A karshen watan jiya hukumomin kasar suka cafke Gamaci Muhammad.
“Shi dai Gamaci an ce dukkan abinda ake tuhumarshi ba laifi ba ne, ba gaskiya ba ne, saboda haka kotu ta ce daga yau an wanke shi.” In ji lauyansa.
Ba sabon abu bane a kasashe masu tasowa musamman ma a Afirka, a ga hukumomi suna fito-na-fito da masu shiga shafin Facebook suna sukarsu.
A daya bangare kuma kotu har ila yau, ta yanke wa wani dan adawa hukuncin zaman wakafi saboda samin sa da laifin cin zarafin mashara’anta a shafin sada zumunta, hukuncin da lauyansa ya ce za su daukaka kara.
Ana zargi Ibrahim Banakasa, kusa a jam’iayr Modem Lumana mai adawa da laifin shiga shafin Facebook ya soki wani hukuncin wata kotu, wanda aka ce ka iya tasiri akan hukuncin da alkalin zai yanke nan gaba a shari'ar.
An yanke mai hukuncin zaman gidan yari na tsawon watannin uku, inda zai kwashe watanni biyu a waje sannan ya kuma yi wata daya a gidan yari.
Tuni Banakasa ya kwashe makwannin uku ya zuwa yanzu, ya rage masa mako guda kenan.
Saurari rahoton wakilin Muryar AMurka Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:
Facebook Forum