Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 8 Sun Mutu A Wajan Kallon Wasan Kwallo


An samu turereniya a wajan kallon wasan kwallon kafa wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 8 inda wasu da dama suka samu raunuka.

Jami'ai a Senegal sun ce mutane 8 sun mutu sannan wasu da dama sun samu raunuka a dandalin wasan a babban birnin kasar a wani turmutsitsin da ya auka yayin wata gasar kwallon kafa.

Ministan Wasannin Matar Ba, ya fadi jiya Asabar cewa turereniyar ta jiya Asabar ta faru ne bayan wata arangama tsakanin bangarorin magoya bayan club-club din da ke karawar wato da US Oukam da State De Mbour a dandalin wasa na Demba Diop da ke birnin Dakar.

Kafafen yada labaran kasar sun ce 'yan sanda sun shiga jefa barkonon tsohuwa kan cincirindon jama'a, wanda ya dada kawo rudami, wanda har ya kai ga faduwar katanga yayin da jama'a ke kokarin ficewar daga dandalin wasan.

Ministan labaran ya yi alkawarin, abin da ya kira "tsauraran matakai ta yadda al'amari irin wannan ba zai kara aukuwa ba."

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG