Yankin Termit, dake da arzikin dazuzzuka masu kunshe da albarkatun dabbobin daji na fuskantar matsaloli dake ciwa hukumomi tuwo a kwarya kamar yadda Kanal Hamza Barmo, daraktan gandun daji na gudumar Tanut ya sheda.
Yana mai cewa dabbobin sun tasauwa karewa sanadiyar yadda mafarauta suka maida farautar sana’a, inda yake cewa masu hannu da shuni na kasar ta jamhuriyar Nijar ne suka karawa harakar kama dabbobin dajin yayi karfi, saboda a cewarsa yawancin masu hannu da shuni suke bukatar dabbobin domin kiwo a gidajensu.
Daraktan ya kara dacewa yanzu haka duk idan suka samu labarin vcewa ana kiwon dabbobin daji alkalin ya basu damar suje gidan domin tabbatar da hakan idan hakan kuma ya tabbata sa a kwashe dabbobin a kuma gurfanar da wanda aka sami dabobi a gidansa.
Kanal Hamza Barmo, ya kuma koka da rashin ingantattun kayan aiki domin su samu su tafiyarda aikin su kamar yadda dokar ta tanada.
Facebook Forum