Mazauna yankin sun ce tankokin yakin Isra’ilar sun bude wuta yayin da suka kutsa kai zuwa wannan yanki na sansanin, daya daga cikin sansanoni ‘yan gudun hijira 8 masu tarihi a zirin Gaza, al’amarin da ya haddasa tsoro a zukatan al’ummar dake zaune a wurin da ma iyalan da suka rasa matsugunansu.
Wani mazaunin yankin, Zaik Muhammad, yace shigowar tankokin yakin yazo musu da matukar bazata.
“Wasu mutanen sun kasa guduwa sannan sun makale cikin gidajensu, suna rokon a kyalesu su fita, a yayin da wasu suka bazama da ‘yan kayan da suke iya dauka a yayin arcewa,” a cewar Muhammad, mai shekaru 25, dake zaune tazarar kilomita daya daga inda aka kai harin, kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters ta kafar sadarwar Chat App.
A yayin da yakin Gaza ke shiga wata na 14, hare-haren Isra’ila na maida hankali a kan yankunan arewaci da tsakiyar Gaza a abin da ta bayyana da samamen hana mayakan Hamas kai mata hari tare da hanasu sake tattaruwa.
An shaidawa dubu dubatan Falasdinawa dasu bar yankunan, abin da ke kara fargabar cewa ba za’a sake barinsu su koma ba.
-Reuters