Falasdinawa a yankin arewacin Gaza suna fama da karanacin abinci bayan wata daya da Isra'ila tayi musu kawanya ba tare da an samu damar shigar da kayakin agajin jinkai ba. Wasu da suka rame a sakamakon rashin abinci sun kaurace daga yankin zuwa birnin Gaza.
Ma'aikatan lafiya a wani asibiti sun sanar cewa dubban yara suna fama da matsanancin matsalar rashin abinci.
Likitoci sun ce matsalar yunwar ta yi kamari.
Sojojin Isra’ila sun zazafa kai hare hare a arewacin Gaza tun daga farkon watan Oktoba. Sun ce suna kokarin kawar da mayakan Hamas ne da suka tare a yankin.
Ana fuskantar wannan yanayin rashin agajin jinkai ne a dai dai lokacin da wa’adin kwanaki 30 da Amurka ta baiwa Isra’ila zai cika zuwa makon gobe. Ta ce dole ne Isra’ila ta bada dama a kara yawan taimakon agajin jinkan da ake shigarwa cikin Gaza ko kuma Amurka ta janye tallafin sojin da take bata.
Dandalin Mu Tattauna