Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Isra’ila Sun Hallaka Mutum 19 A Lebanon


Wani gini da Isra'ila ta kai wa hari a kudancin Lebanon a ranar 23 ga watan Oktoba 2024.
Wani gini da Isra'ila ta kai wa hari a kudancin Lebanon a ranar 23 ga watan Oktoba 2024.

“Duk birnin ya firgita, kowa na kokarin sanin inda zai je; akwai cunkoso sosai,” in ji Bilal Raad, shugaban ceto na Lebanon na shiyya Bilal Raad, kamar yadda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Hare-haren da jiragen saman Isra’ila suka kai kan birnin Baalbek mai tsohon tarihi a gabashin Lebanon a ranar Laraba sun kashe mutum akalla 19, a cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon.

Sa’o’i kafin hare-haren, sojojin Isra’ila sun bayar da umarnin kowa ya fice daga birnin gaba daya da wasu yankunan Kogon Bekaa na gabashin Lebanon, inda Baalbek ke nan.

Dubban mutanen Lebanon sun yi ta ficewa cikin firgici da rudani, in ji wani jami’in ceto na Lebanon.

“Duk birnin ya firgita, kowa na kokarin sanin inda zai je; akwai cunkoso sosai,” in ji Bilal Raad, shugaban ceto na Lebanon na shiyya Bilal Raad, kamar yadda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Baalbek shi ne wurin da ake dauke da wurin ibadar Roma wanda ke cikin jerin wuraren tarihin duniya na UNESCO.

A gargadin da ta yi Isra’ila ta ce tana kaikaitar Hezbollah ne.

Isra’ila kan ba da irin wadannan umarnin ficewa kafin hare-haren soja a yakin da take yi da Hamas a Zirin Gaza.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji sun yi suka kan umarnin ficewa, suna cewa ’yan kasa na da karancin damar shiri kuma yawanci babu wani wurin tsira da za su je.

Shugaban Amurka Joe Biden da Shugaban Cyprus Nikos Christodoulides sun hadu a Fadar White House a ranar Laraba don tattauna yadda za a kawo karshen fada a Lebanon da Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG