Sojojin Da Suka Yi Tawaye A Gabon, Sun Nada Jagoran Soja Bayan  Sun Tsare Shugaban Kasar

Sojojin rike da Janar Brice Clothaire Oligui Nguema daga sama a Libreville, Gabon, Aug. 30, 2023. (Gabon24 via AP)

Sojojin da suka yi tawaye a Gabon, sun bayyana shugaban dakarun tsaro na kasar a matsayin shugaban kasa, bayanda suka yi wa Shugaban kasar da aka zaba a kwanan nan, Ali Bongo Ondima daurin talala a gidan sa.

Sojojin sun zarge shi da laifin cin amanar kasa da almubbazzaranci a tsowon mulkin shi na kasar mai arzikin mai dake tsakiyar Afrika

Jagororin juyin mulkin sun sanar cikin wata sanarwa ta kafar talbijin din kasar cewa, baki daya an amince da janar Brice Clotaire Oligui Nguema, ya shugabanci kwamitin rikon kwaryar da zai jagoranci kasar. Oligui wanda dan’uwa ne ga Bongo, wanda aka bayyana ranar Laraba, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na baya bayan nan, bayan shafe shekaru 55 suna jan akalar kasar, shi da mahaifin shi.

Janar Brice Oligui Nguema

A cikin wani faifan bidiyo da ya nuna shi daga inda yake tsare a gidan shi, Bongo yayi kira ga jama’a dasu daga murya su goyi bayan shi. To sai dai, maimakon hakan, dandazon mutanen da suka bazu bisa hanyoyin babban birnin kasar, sun rika nuna farin cikin su ne da juyin mulkin da aka yiwa tsarin gidan sarautar da aka zarga da kara azircewa daga dukiyar kasar, yayinda dimbin al’ummar kasar ke fama da hakilo.

Shugaban Gabon, Ali Bongo Ondima

Jagororin juyin mulkin sun ce, akwai dokar takaita zirga zirgar jama’a daga karfe 6pm na yamma zuwa karfe 6 am na safe, lokacin kasar, amma za’a kyale mutane yin zirga zirga ba tare da wata tsangwama ba a rana a ranar Alhamis.

A ranar Laraba, Lt. Col. Ulrich, shugaban rikon kwaryar, ya jaddada ta kafar talbijin din kasar, bukatar dake akwai, na cigaba da kasancewa a natse cikin kwanciyar hankali a kasar mu, yace, “a farkon wani sabon karni, zamu bada tabbatcin samar da zaman lafiya, daidaito da yanci na abin kaunar mu, Gabon.”

Sabon shugaban sojan, Oligui a baya ya kasance jami’in dake kare mahaifin Bongo, marigayi shugaba Omar Bongo, inji danjarida Desire Emma, dake aiki da wata kafar yada labarai ta Echos du Nord. Haka zalika, Oligui ya taba jagorantar hukumar liken asirin kasar a shekarar 2019, kafin daga bisani ya zama shugaban dakarun republican.

Sojojin juyin mulki a Libreville, Gabon (GABON 24 via AP)

Ali Bongo Ondimba, mai shekaru 64 a duniya, ya shugabanci kasar har sau biyu, tun bayan da ya dare karagar mulki a shekarar 2009 bayan mutuwar mahaifin shi, wanda ya mulki kasar har tsawon shekaru 41,, inda aka danganta mulkin shi da al’amurra marasa dadi.. Ko a shekarar 2019 sai da wasu fandararun sojojin suka yi yunkurin juyin mulki, amma aka murkushe shi cikin sauri.

Kasar dake cikin kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka, mamba ce ta kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, OPEC, amma arzikin man ya tattaru ne a hannun wasu yan tsiraru, inda kusan kashi 40 daga cikin 100 na ‘yan kasar Gabon dake tsakanin shekara 15 zuwa 25 suka rasa aikin yi a shaekarar 2020, a cewar Bankin duniya. Kudin da kasar ke samu daga man da take fitarwa waje yana dalar Amurka bilyan 6 ne a shekarar 2022, kamar yadda bayanan hukumar makamashi ta Amurka ta sanar.

A halin yanzu dai ana gudanar da bincike, a kasar Faransa, kan iyalan Bongo su 9,, inda wasu ke fuskantar binciken farko kan zargin almubbarzaranci, a cewar kungiyar Sherpa dake bin diddikin tabbatar da yin gaskiya, mai zaman kanta dake Faransa. Masu bincike sun alakanta iyalan da kadarori na sama da dala milyan 92 dake Faransa, da suka hada da fadoji biyu a garin Nice, a cewar kungiyar.

~Hauwa Sheriff