Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Nada Sabbin Gwamnoni

Masu goyon juyin mulkin Nijar (AP)

Haka kuma majalisar sojojin ta sanar da bude iyakokin kasar ta Nijar da wasu kasashen da ba su da alaka da ECOWAS.

NIAMEY, NIGER - Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijer sun nada gwamnonin jihohi 8 na kasar a ci gaba da yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya.

Haka kuma majalisar sojojin ta sanar da bude iyakokin kasar ta Nijar da wasu kasashen da ba su da alaka da ECOWAS.

Hakan na zuwa ne a yayin da a ke sa ran wata tawagar masu shiga tsakani ta ECOWAS/CEDEAO za ta kai ziyara kasar ta Nijar a ranar Laraba don tuntubar bangarorin da ke takaddama.

A sanarwar da suka bayar ta kafar talbijan mallakar gwamnatin Nijar ne suka sanar da jama’ar kasar nade-naden sabbin gwamnonin.

Hafsoshin soja ne aka nada domin maye guraben gwamnonin hambarariyar gwamnatin wadanda suka hada da Janar-Janar guda hudu da Kanal biyu da Kontrolan ‘yan sanda daya da kuma Laftanal Kanal guda.

A halin da ake ciki, 'yan Nijar sun fara tofa albarkacin bakin dangane da wannan mataki na nada gwamnonin kasar.

Wani ‘dan kasa Tchanga Tchalimbo na cewa wadanan nade-nade alama ce ta fatali da tayin sulhu alhali ita kadai ce mafitar halin da Nijar ta tsinci kanta ciki.

Tuni dai al’umma ta fara dandana radadin takunkumin da kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta kakaba wa kasar inda farashin kayan abinci ya yi tashin gwaron zabi, misalin yadda bahun kg 25 na shinkafa da ke jaka 10 na cfa a baya(10000f) ya koma jika 15 (15000f).

A bankuna ma an fara fuskantar tsaikon hada-hada inda masu kokarin cire kudade ke cincirindo a wani lokacin da aka fara fuskantar karancin masu ajiya saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya zo.

Haka kuma an shiga matsalar wutar lantarki sanadiyar tsinke layin da Najeriya ta yi a wani lokacin da wasu mambobin Majalisar CNSP suka fara rangadin kasashe makwafta wato Mali da Burkina Faso.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Sun Nada Sabbin Gwamnoni 6.mp3