Jakadan ya ce zargin cewa tsaro na tabarbarewa kuma tattalin arzikin kasa ba ya cigaba, duk karya ce. Sun kuma san ba daidai ba ne.
Ya ce Nijar ta yi ta samun nasarori daban-daban.
A cewarsa, bai ko wuce sati daya ba da tawagar manya-manyan sojojin duniya su ka zo nan ba, su ka yi taro, su kuma su ka tafi tare zuwa Pentagon, shi ya sa da mamaki a ce a wayi gari, a ce wai ba a cin nasara a kasar.
Ya kara da cewa ko a karon farko cikin shekaru 15 da suka wuce, an kammala karatun shekara ba tare da yajin aikin kwana ko daya ba.
Saboda haka, babu wani tashin hankali ko daya da zai bada dalili ko hujja da za a ce za a zo a yi yunkurin mulki.
"Wannan yunkurin na son kan mutum daya ne kawai." in ji shi.
Game da matakin ECOWAS kan Nijar, Jakadan ya ce ECOWAS ba ta taba daukan tsatsauran matakai kaman wannan ba, kuma ta yi ne saboda wannan yunkurin juyin mulkin, ba ta da wata hujja ko kaɗan, la'akari da nasarorin da Nijar ta ke ta samu.
Saurari cikakken hirarsa a sauti:
Dandalin Mu Tattauna