Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mali, Burkina Faso Sun Yi Gargadi Kan Daukan Matakin Soji A Nijar


Shugaban mulkin soja na kasar Mali, Colonel Assimi Goita
Shugaban mulkin soja na kasar Mali, Colonel Assimi Goita

A yayin da gwamnatin Faransa ta ayyana shirin kwashe ‘yan kasarta daga Nijar, kasashen Mali da Burkina Faso sun jaddada goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.

NAIMEY, NIGER - Gwamnatin sojin kasashen Mali da Burkina Faso, sun aika da sakon gargadi ga kungiyar ECOWAS/CEDEAO kan shirin da take yi na daukan matakin soji a Jamhuriyar Nijar.

Kasashen na Mali da Burkino Faso sun ayyana cewa amfani da karfin soja wajen mayar da hambararriyar gwamnati tamkar ECOWAS ta ja su yaki ne.

Hakan a cewar na nufin za su kafsa da duk wata kasar da ke da niyyar aiwatar da abin da suka kira mummunan mataki akan makwabciyarsu Nijar.

Rashin aminta da jerin takunkumin da kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta kakaba wa sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar ya sa gwamnatocin rikon kwaryar Mali da Burkina Faso fitar da sanarwar hadin guiwa.

Sanarwoyin wadanda aka bayar ta kafafen labarai mallakar gwamnati sun jaddada goyon baya ga al’ummar Nijar a abinda suka kira yunkurin ceto kansu daga hannun ‘yan mulkin mallaka saboda haka ba za su zartar da matakan na ECOWAS akan ‘yan uwansu ‘yan Nijar ba.

Kakakin gwamnatin Mali, Colonel Abdoulaye Maiga, ya ce suna kashedi akan yunkurin daukan matakin soja kan Nijar domin yin haka tamkar an tsokani kasashen Burkina Faso da Mali yaki ne. Kuma yin hakan abu ne da zai sa wadanan kasashe su fice daga kungiyar CEDEAO.

Nijar kasar da galibin kayan abinci da dukkan ababen masarufi ke shigo ta daga waje sakamakon rashin tashar jirgin ruwa ta kashin kanta na iya fuskantar koma bayan a sanadiyar hukuncin na CEDEAO, ‘dan rajin kare dimokradiya Souley Oumarou na kungiyar FCR na da damuwa akan yadda abin ka iya karewa akan talaka ne.

Wannan dambarwa ta tsakanin Mali da Burkina Faso da sauran kasashen ECOWAS al’amari ne da masana sha’anin tsaro ke ganinsa tamkar wani tarnaki a yaki da ‘yan ta’addan yankin sahel, abinda Dr. Seidik Abba na mai jan hankuli a kai.

A yanzu haka kasar Faransa ta hanyar ma’aikatar harkokin wajenta ta sanar na shirin kwashe ‘yan kasarta da ma dukkan ‘yan nahiyar turai da ke bukatar ficewa daga Nijar.

Hakan na zuwa ne bayan harin da wasu masu zanga zangar goyon bayan juyin mulkin a ranar 26 ga watan Yuli suka kai kan ofishin jakadancinta a Yamai a yayin da aka shiga wuni na biyu a wa’adin mako guda da CEDEAO ta bai wa sojojin CNSP su saki hambararen shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ko kuma ta yi amfani da karfin soja.

Saurari ciakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Mali, Burkina Faso Sun Yi Gargadi Kan Daukan Matakin Soji A Nijar.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG