Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Sake Bude Iyakokinta Da Wasu Makwabtanta


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Jumahuriyar Nijar ta sake bude kan iyakokinta da wasu makwabtanta, mako guda bayan juyin mulkin da ya girgiza yankin Sahel na yammacin Afirka.

WASHINGTON, D.C. - "An sake bude iyakokin kasa da na sama tsakanin Aljeriya, Burkina Faso, Mali, Libya da Chadi daga 1 ga Agusta, 2023," in ji kakakin mulkin sojan kasar Kanal Amadou Abdramane a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta rufe iyakokin kasar, a daidai lokacin da ta bayyana cewa ta sauke zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum daga kan karagar mulki.

Kungiyar ECOWAS ta yankin ta kakaba takunkumi, da suka hada da dakatar da duk wasu harkokin hada-hadar kudi da kuma dakile kadarorin kasar, kuma ta ce za ta iya ba da izinin yin amfani da karfin soji don maido da Bazoum.

Sai dai mahukuntan kasashen Burkina Faso da Mali da ke makwabtaka da Nijar sun bayyana goyon bayansu ga jagororin juyin mulkin inda suka ce duk wani tsoma-bakin waje na maido da hambararren gwamnatin da ake kokarin yi, za a yi masa kallon neman yaki.

Wannan sanarwar da Mali da Burkina Faso suka yi a daren ranar Litinin ta nuna cewa wata kila wata sabuwar kawance ta kulla dabam a tsakaninsu ba da sauran kasashe 15 na kungiyar ba.

A halin da ake ciki kuma, a yau Laraba ne jiragen soja na farko dauke da ‘yan kasashen Turai da aka kwashe daga Nijar suka sauka a birnin Paris da Roma.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG