Yanzu haka a jihar Taraba an fara musayar kalamai tsakanin mukarraban gwmanan jihar Danbaba Suntai, da kuma bangaren mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar.
WASHINGTON, D.C —
Sai dai mukarraban gwamnan jihar na korafin cewa an yi mishi talala, saboda an takaita wadanda zasu ringa kai masa ziyara, lamarin da suka ce ba zai yiwu ba.
Senata Emmanuel Buacha dan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar Taraba ta Kudu, kuma na gaban Suntai yace canza jami’an tsaron dake gadin gwamnan, yunkurin kwace mulki ne.
“Yayi kokarin ya kwace mulki daga wurin gwamnan, amma abun bai yiwu ba” a cewar Senata Emmanuel.
Senatan ya kara da cewa “Mun samu labarin yana cancanza jami’an tsaro wadanda suke cikin gidan gwamna”.
Rigingimun siyasa dai a jihar Taraba na cigaba ne tun bayan da gwamnan jihar Danbaba Suntai yayi hatsarin jirgin sama a bayannan.
Ga labarin a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5