Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Yayin da ake ganin dambarwar siyasar jihar Taraba ta kawo karshe sai gashi Ubangiji Ya yiwa Kakakin Majalisar Dokokin jihar rasuwa

Tun da gwamna Danbaba Suntai ya dawo daga jinya bayan ya samu hatsarin jirgin sama jihar ta shiga cikin halin rudani domin gwamnan wanda ya ki ya bayyana a bainar jama'a ya nemi ya koma kan aikinsa.

Majalisar jihar a karkashin shugabancin Haruna Tsokwa ta ki ta amince da bukatar gwamna Suntai. A madadin haka sai ta tsayar da doka inda ta yarda mukaddashin gwamnan ya cigaba da rike madafin iko har sai gwamna Suntai ya murje.

Matsayin majalisar ya sa gwamna Suntai ya garzaya kotu inda yake neman a mayar masa da ikonsa. Makon jiya a ka ji cewa an samu sulhu har ma shi mukaddashin gwamnan ya gabatar da sunayen sabbin kwamishanoni da suka hada da wadanda gwamna Suntai ya zaba.

Ana jiran aji ko majalisar zata amince da sunayen da mukaddashin gwamnan ya mika mata sai kawai yau aka sanarda rasuwar kakakin majalisar Haruna Tsokwa bayan rashin lafiyar kwana biyu kacal.

Domin tabbatar da gaskiyar labarin abokiyar aiki Halima ta zanta da wakilin Muryar Amurka a jihar Taraba Ibrahim Abdulaziz. Ya tabbatar cewa yau da safe kakakin majalisar Haruna Tsokwa ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya ta kwanaki biyu. A halin da ake ciki ana kokarin daukar gawarsa zuwa gida. Inji shi Ibrahim rasuwar ta jefa jihar cikin wani halin rashin tabbas domin ta faru daidai lokacin da majalisar zata fara duba sunayen da mukaddashin gwamnan ya gabatar mata.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:58 0:00
Shiga Kai Tsaye



LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”
XS
SM
MD
LG