To sai dai wani sabon yunkurin da mukaddashin gwamnan ya yi wata alama ce cewa kamar an kawo karshen dambarwar. Mukaddashin gwamnan ya mika sunayen wadanda yake so ya nada kwamishanoni. Sunayen sun hada da na bangaren Gwamna Danbaba Suntai da tsofofin kwamishanoni da suka balle da na bangaren mukaddashin har ma da wanda bangaren Suntai ya nada a matsayin sakataren gwamnati Barrister Timothy Katas.
Mukddashin gwamnan ya godewa jama'ar jihar da kai zuciya nesa dangane da abubuwan da suka taso. Ya ce sun yi anfani da hankalinsu. Sun zuba ido suga yadda abubuwa ke gudana. Mukaddashin ya ce bayan hakan sun ci gaba da addu'a kuma Allah a cikin jinkansa ya kawo saukin abun. Ya ce yanzu sun sasanta da juna. Ya cigaba da ba al'umma hakuri cewa yadda suka rike juna su cigaba da yin hakan domin cigaban jihar. Ya ce yanzu kam gwamnati zata tashi ta yi aiki wurjanjan a ga cewa kowa ya samu abun da ya cancanta. Ya ce zai cigaba da tattaunawa da maigidansa wato gwamna Suntai su san wadanda yakamata su kawo cikin gwamnati.
Tuni wasu 'yan jihar suka soma mayarda martani dangane da matakin da mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umaru ya dauka. Honorable Markus Haruna wanda ya rike mukamai da yawa a jihar ya ce jihar Taraba bata da matsalar addini. Abun da ya faru shi ne wadansu mutane ne da suke son biyan bukatan kansu suke neman kawo tashin hankali.
Ga karin bayyani.