Rikicin ya faru ne tsakanin al'ummomi biyu na kabilar Tiv dake makwaftaka da jihar Binuwai. Malam Hodu Mohammed Donga ya kara haske kan lamarin. Ya ce rikicin ya faru ne tsakanin Tiv dake Agabi cikin yankin Donga da kuma Tiv dake Agbako kan hanyar zuwa Takum. Ya ce akwai wani wanda da babban dan fashi ne amma ya tuba kuma yana tona asirin sauran barayi wadanda suke damun al'ummomin yankin. Shi barawon da ya tuba dan kabilar Ogondo ne amma yana tona asirin barayin kabilar Ikire sanadiyar rigimar ke nan
Sarkin Donga Dr Danjuma Stephen Bayonga ya taba kiran kabilun ya ja kunnensu su zauna lafiya ya ce baya son rigima a masarautarsa. To sai gashi rikicin da sarkin ke gudu ya faru har ya hallaka mutane goma sha biyar da dukiyoyi.
An tura sojoji da 'yansandan kwantar da tarzoma yankin domin kwantar da hankula yayin da mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Umaru Garba ya kira al'ummar yankin su kwantar da hankula. Mr. Kefas Sule sakataren yada labarai na mukaddashin gwamnan ya bayyana matakan da aka dauka. Ya ce 'yansanda da sojoji sun shiga yankin da umurnin mukaddashin gwamnan su rika sintiri a yankin dare da rana domin a tabbatar rikici bai sake tashi ba a yankin.
An ambato cewa gidaje da yawa aka kona sabili da haka ne kakakin 'yansandan jihar Joseph Kwaji ya ce za'a hukumta duk wadanda ke da hannu a cikin rigimar. Ya kira jama'a a zauna lafiya da kashedin a daina yayata jita-jita.
Kawo yanzu 'yan gudun hijirar da abun ya shafa suna cigaba da kwarara zuwa garin Donga da wasu kauyuka dake makwaftaka da yankin.
Ga rahoto.