Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaron Yankin Sahel A Nijar

Shugabanin Hukumomin Tattara Bayanan Sirri A Yankin Sahel Sun Gudanar Da Taro A Nijar

Shugabannin hukumomin kula da tattara bayanan sirri sun gudanar da taro a karkashin inuwar kwamitin kwararru na MDD, wanda  tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou ke jagoranta don neman mafita ga matsalolin tsaro da ayyukan ci gaban al’umma a yankin Sahel.

NIAMEY, NIGER - Mahalartan wannan taro na kwanaki biyu sun tattauna hanyoyin musanyar bayanai domin karfafa matakan tsaro a kan iyakokin kasashen yankin Sahel.

Shugabanin Hukumomin Tattara Bayanan Sirri A Yankin Sahel Sun Gudanar Da Taro A Nijar

Kasashe a kalla 16 ne suka hadu a wannan taro domin bitar halin da ake ciki a fannin tsaro a yankin na Sahel, abin da ya bai wa gomman mahalartan dukkansu shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri damar tattauna hanyoyin da za su taimaka wa yunkurin karfafa matakan sa ido a kan harkokin ‘yan ta’adda musamman akan iyakokin kasashen.

Tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou, wanda shine shugaban kwamitin MDD mai kula da tsaro da ayyukan ci gaba a yankin Sahel, ya bayyana makasudun kiran wannan haduwa da tasirin maudu’in da aka baje akan teburi a tsawon kawanki biyu.

Ya ce abokin gabar da muke yaka ba ya zama wuri guda ya na kai da kawowa a tsakanin iyakoki, saboda haka barazana ce da ta shafi duk kasashen. A sansanonin yankin Sahara da Sahel da yankin tafkin Chadi a yau barazanar abokan gaba ta yadu zuwa kasashen gabar tekun Guinea, abin da ya sa a yau hankulan duniya ya karkata kan wadanan yankuna, saboda haka ya zama wajibi kowace kasa ta karfafa matakan tsaro da na samar da bayanan sirri, haka kuma ya zama wajibi a kasashe su yi musanyar irin wadanan bayanai.

Shugabanin Hukumomin Tattara Bayanan Sirri A Yankin Sahel Sun Gudanar Da Taro A Nijar

Taron wanda shine makamancinsa na farko da ke hada shugabanin hukumomin tattara bayanan sirrin kasashen Sahel da mambobin kwamitin koli na MDD mai kula da neman hanyoyin warware matsalolin tsaro da samar da ci gaban al’umma a wannan yankin, abu ne da shugaban hukumar tattara bayanan sirri na tarayyar Najeriya Ahmed Rufa’I Abubakar ya ce zai kara masu kwarin guiwa a huldar da ta shafi musanyar bayanai a tsakanin kasashe.

Shugaban kwamitin koli na MDD mai alhalin zakulo hanyoyin warware matsalolin tsaro da samar da ci gaban al’umma a yankin Sahel Issouhou Mahamadou, ya yaba wa wasu cibiyoyin tattara bayanan sirri wadanda suka hada da UFL ta kasashen Sahel da Regional Inteligence unit RUFI ta yankin tafkin Chadi da Security Service of Afrika CISSA da Centre Africain d’etudes et de Recherche sur le Terrorisme CAET saboda rawar da ya ce su na takawa a yaki da ta’addanci ta hanyar ingantattun bayanan sirrin da suke bayarwa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabanin Hukumomin Tattara Bayanan Sirri A Yankin Sahel Sun Gudanar Da Taro A Nijar .mp3