NIAMEY, NIGER - A yankin Sahel ne dai kungiyoyi masu tada kayar baya ke yada labaran karya domin haddasa rudani tsakanin jama’a. Gonzolo ya na mai jaddada aniyar ci gaba da wannan aiki na hadin gwiwa domin samun nasara.
Gonzalo Suarez wanda ke ziyarar aiki a Nijar ya tattauna da Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou a game da batun tsaro a kasar, da kuma yankin Sahel inda Amurka ke taka rawa sosai wajen ganin an kawo karshen ayyukan ta’addancin da suka hana jama’a sakat a shekaru da dama.
Ya ce mun tattauna akan babban hadarin da ake fuskanta a fannin tsaro a wannan yanki wanda kuma ke da nasaba da yada labaran karya da a wani gefe aika-aikar ‘yan kungiyoyin ta’addanci ne dake kan iyakokin Nijer.
Ya kara da cewa, za mu ci gaba da aiki da Nijar a fannin tsaro da diflomasiyya da ayyukan ci gaban al’umma har sai mun cimma burinmu na tabbatar wa ‘yan ta’adda cewa ba za su taba samin matsuguni ba a wannan yanki.
Mataimakin karamin sakataren Amurka mai kula da sha’anin tsaron kasa da kasa din ya bayyana gamsuwa da abinda ya kira jajircewar hukumomin Nijar akan maganar samar da tsaro.
Gonzalo Suraez ya kara da cewa na yi farin cikin ji daga bakin Firai Minista irin matakan da hukumomin Nijar ke dauka domin samar da tsaron kasa da kasa.
Nijar da Amurka na gudanar da ayyukan hadin gwiwa wadanda ke karkashin kulawar ma’aikatata, ya kuma ce muna godiya sosai da Firai Minista ya bamu damar yin wannan tattaunawa, zaman nan da muka yi hujja ce da ke nunin hulda ta gaskiya da ke tsakanin Amurka da Nijar.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma: