Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Afrika Ta Yamma Na Kokarin Dakile Ta'addanci A Yankin Sahel


Shugabannin ECOWAS
Shugabannin ECOWAS

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da su kara kaimi wajen kawo karshen ta'addanci a yankin.

Shugaban ya yi gargadin cewa yawan tashe-tashen hankula a yankin Sahel da wasu kasashen yammacin Afirka na barazanar mamaye yankin baki daya, babu wata kasa da ta tsira har sai an kawo karshen ayyukan ta'addanci a cewarsa.

Akufo-Addo ya fadi hakan ne a wajen wani taron shugabannin kasashe bakwai a yammacin Afirka da suka hada da Benin, Togo, Burkina Faso, Ivory Coast, Niger, Mali da Ghana. Taron da aka fi sani da "The Accra Initiative," an yi shi ne a birnin Accra da nufin kulla alaka mai karfi don tunkarar matsalar ta'addanci a yammacin Afirka da yankin Sahel.

Shugabannin ECOWAS
Shugabannin ECOWAS

Da yake jawabin bude taron, mai amsar baki kuma shugaban taron Nana Akufo-Addo, ya bayyana cewa taron ba kawai zai tantance da kuma gano kalubalen tsaro da ke fuskantar yankin yammacin Afirka ba ne, zai kuma fitar da hanyoyin magancesu.

“Yammacin Afirka na ci gaba da fama da matsalar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da ke yaduwa cikin sauri a duk fadin yankin. A yau, kungiyoyin 'yan ta'adda sun samu kwarin gwiwa saboda nasarar da suka samu a yankin kuma yanzu suna neman sabbin hanyoyin fadada ayyukansu, lamarin da ya janyo tabarbarewar tsaro a yankin Sahel har zuwa yankin gabar tekun yammacin Afirka,” a cewar shugaban.

Shugabannin ECOWAS
Shugabannin ECOWAS

Hare-haren ta'addanci sun karu cikin shekaru goma da suka gabata a yankin, duk da kokarin da ake yi na yaki da masu tada kayar baya. Rikicin da ya yi sanadiyar salwantar dubban rayuka tare da raba mutane sama da miliyan biyu da dubu dari bakwai da muhallansu a fadin yankin Sahel, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Haka kuma, sama da mutane miliyan talatin a yankin Sahel za su bukaci taimakon gaggawa da kariya a shekarar 2022, kusan miliyan biyu fiye da adadin da aka gani a shekarar da ta gabata. Kasashen da ke gabar teku irinsu Benin, da Togo na fuskantar karuwar hare-hare a shekarun baya-bayan nan.

Kasashen yammacin duniya kamar Burtaniyya, Faransa, da Jamus na janyewa daga ayyukan wanzar da zaman lafiya a Mali, lamarin da ka iya ta'azzara matsalar tsaro a yammacin Afirka.

Mista James Heappey, ministan sojan kasar Burtaniyya, ya fadi cewa sun san akwai kalubalen tsaro kuma sun riga sun samu kyakkyawar alaka da kasashen Afirka, bayan haka a shirye suke su taimaka ta kowace hanya da za su iya. Sai dai, “ba mu ke da amsar matsalolinku ba, a cewarsa. Kuma ba za mu nuna kamar muna da duk amsoshin matsalolinku ba. Kuna da amsa, kuna da mafita, kuma kuna da tsari.”

Heappey yace kasarsa da sauran kasashen yammacin duniya za su ci gaba da kasancewa kawaye kuma abokan huldar kasashen yammacin Afirka wajen yaki da ta'addanci da tsattsauran ra’ayi amma ba za su nuna musu yadda za su magance matsalolinsu ba.

Shi ma Irbad Ibrahim, masani a kan tsaro da hulda tsakanin kasa da kasa, yace ya zama wajibi gwamnatocin wannan yanki su samarwa matasa aikin yi, da jan hankali kan kaucewa kalaman tsattsauran ra’ayi a masallatai, da kokarin daidaita bambancin akida tsakanin addinai, da dai sauransu.

A wani lamari da ke da alaka da wannan, gwamnatin Ghana ta musanta rahotannin da ke cewa ana kawo dakaru na musamman daga kasar Burtaniyya zuwa Ghana domin taimakawa wajen yaki da ta'addanci.

Wani rahoto da jaridar "The Telegraph" ta kasar Burtaniyya ta fitar ya nuna cewa Burtaniyya na tattaunawa da Ghana domin tura dakaru na musamman cikin kasar bayan da aka tilasta mata janye daukacin dakarunta na kiyaye zaman lafiya a Mali.

"Gwamnatin Ghana na son bayyana cewa labarin da ke yawo game da dakarun Burtaniyya na musamman ba gaskiya ba ne," a cewar wata sanarwar ma’aikatar kasashen wajen Ghana. Babu wani mamban Accra Initiative ko kasar Ghana da ya tattauna da kasashe abokan hulda kan wannan bukatar, ko ma tunanin shigar da wasu dakarun kasashen waje a harkokin yankin. Domin haka, gwamnati ba ta da wata yarjejeniya da kasar Burtaniyya kan kai dakaru Ghana.

Saurari rahoton Idriss Abdullah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

XS
SM
MD
LG