Shugaban kungiyar matasa ta APC youth vanguard ta kasa Abdullahi Ciroma, ya ce jama’a su fahimci cewa siyasa ce tsagawaronta ake yi a majalisar domin karkatar da hankali daga canjin da jama’a suka zabarma kawunansu.
Ya ce kawunan sauran kabilun Najeriya hade yake da zarar sun shiga majalisa duk da bambancin siyasa da addini dake tsakanin su, kuma gashi wannan sabuwar gwamnati ta hada kan manyan addinan kasar da samar da jituwa tsakanin manyan kabilai da kanana saboda a samu a zauna lafiya.
A mayar da martani kan tambayar da wakilyar sahsen Hausa Zainab Babaji ta yi masa cewa ina nasabar rigingimun ‘yan majalisa da talakawa, shugaban matasan ya bayyana cewa idan majalisa bata zauna lafiya ba, babu yadda za’ayi masu zartarwa su sami sukunin aiwatar da ayyukan su.
A cewar sa, makiya jam’iyyar ne k enema su dagula al’amarin gwamnatin domin shugaban kasa ya duba kasafin kudin bayan kiran da jama’a sukai tayi, dan haka neman dagula lamarin kawai suke bukatar yi.
Itama shugabar kungiyar dake tallafawa marayu da gwauraye wato CAWA, Maryam Alexander ta yi kira ne domin a hada kai saboda samun kyakkyawan ci gaba.
Sakatariyar kungiyar mata magoya bayan jam’iyyar APC a arewa Ladi Sani Gangare ta jaddada cewa kamata yayi shugabannin jam’iyyar APC na kasa su sa baki domin warware wannan takaddama dake majalisar.
Majalisar wakilan ta shiga dambarawar ne a sakamakon zargin aringizo a kasafin kudi.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5