Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauwa Liman: Abu Daya Zuwa Biyu Matasan Najeriya Ke Bukata!


Hauwa Liman
Hauwa Liman

Hauwa liman, na daya daga cikin matasa 'yan kasashen Afrika, da shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya gayyata. Ta bayyanar da irin yadda taga matasa a kasar nan ke kokarin dogaro da kansu, batare da suna jiran gwamnati ko wani ba. A iya zaman ta na makonni shida, ta hadu da matasa da suka fara sana'o'i tun bayan kammala karatun su na sakandire, wanda suka zama masu kudi bama kadan ba. Shiri ne na horas da matasan Afrika akan shugabanci, sana'o'i da hada-hadar kasuwanci, da inganta aikin gwamnati. A halin yanzu suna samun horo a nan kasar Amurka.

Hauwa, na ganin cewar idan har matasa zasu daina dogaro da gwamnati da tashi tsaye wajen ganin sunyi ma kansu abun da ya dace, to ba mamaki kasar Najeriya, sai tafi kowace kasa a fadin duniya. Domin kuwa matasan Najeriya, ba raggwaye bane, kawai abun da suke bukata shine su samu masu basu shawara ta yadda zasu gudanar da abubuwan su na yau da kullun.

Har ila yau, Hauwa ke jagorantar matasan da ke yunkurin kafa IMPACT AREWA, wanda shiri ne da zai tabo bangarori daban-daban da sukewa matasan Arewa illa da kawo cikas ga cigaban matasan. Don haka wannan horaswar da suka samun suna fatar suyi amfani da shi, wajen ganin sun taimaka da bada shawarwari ga kowane matsahi ko matashiya da suka nuna sha'awar su ta neman dogaro dai kai a gida Najeriya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG