Dalibai ‘yan asalin jihar Neja dake karatu a kasar Masar sun nuna damuwa akan rashin samun tallafi daga gwamnatin jihar ta.
A wani taron manema labarai a Mina fadar jihar gwamnatin ta jihar Neja, daya daga cikin shugabannin kungiyar daliban malam Muhammadu Bello Musa, ya ce duk da yake sun dade suna mika kokon bararsu ga gwamnatin jihar kan neman gwamnatin ta taimaka masu, amma har yanzu babu wani bayani.
Malamin ya kara da cewa daliban jihar dake karatu a kasar Masar musamman wadanda ke cikin birnin Al-kahira sun kai kusan 100, kuma suna fuskantar kalubale iri iri kama daga litattafai zuwa wurin zama a bakuwar kasar.
Koda shike kokarin jin ta bakin kwaminiyar ma’aikatar ilimin jihar Hajiya Fatima Madugu, yaci tura, amma sakataren labaran gwamnan jihar Jibril Baba Nda, ya ce duk dan jihar Neja dake karatu a waje ya kara hakuri zai sami taimako daga gare su, domin a cewar sa ba anyi haka dan a kuntata masu bane.
Masana harkokin ilimi sun bayyana cewa taimakawa dalibai na daya daga cikin hanyoyin bunkasa harkokin ilimi.