Wasu daruruwan matasa maza da mata sun gudanar d zanga zanga domin nuna takaicin su akan rashin samun wutar lantarki a jihar Neja.
Masu zanga zangar sun datse babbar kofar shiga gidan gwamnatin jihar dake Mina, dauke da kwalayen dake nuna rubuce rubucen dake nuna macin rai akan rashin wutar tare da rera wokoki.
Yahaya Hussaini Ibrahim, shine ya jagoranci tawagar matasan kuma yayi Karin bayanin cewa abinda ya sa su yin zanga zangar shine ganin yadda suke da manya manyan dam har guda uku wadanda suke samar da wutar lantarki amma basa samunta. Ya kara da cewa rashin wutar yayi sanadiyyar rasa ayyukan yi ga matasa da dama.
Bayan kimanin sa’a guda da matasan ke datse da babbar kofar shiga gidan gwamnatin, mataimakin gwamnan jihar Alhaji Muhammad Ketsu, ya fito inda yayiwa matasan alkwarin cewa gwamnatin jihar na bisa kan kokarin tattaunawa domin ganin yadda zata shawo kan lamarin.
Jami’in yada labarai na kamfanin samar da hasken wutar lantarki dake Mina Adamu Muhammed Pele, ya ce matsalar hare haren da tsagerun Niger Delta ke kaiwa akan butatan man kasar ne ya haifar da rashin samun wutar lantarkin.
Bincike ya nuna cewa akwai jama’a da dama da suka koma hannu rabbana a sakamakon rashin wutar lantarki domin sana’o’in sun a dogaro ne da wutar lantarki.
Saurari cikakken rahoton a nan.