Ana gobe ranar zagayowar cika shekaru 55 da haihuwar shugaba Obama, sai gashi anyi masa maraba da wakar murnan wannan rana daga dubban matasan dake halartan taron shugabannin manyan gobe na ‘yan Afifka na wannan shekarar da ake yi anan washington.
Shugaba Obama dai shine ya kaddamar da wannan kungiyar ta manyan gobe na Africa (YALI ) Wanda daga baya yayi mata lakabi da kungiyar zumunci ta Mandela Washington.
Ya samar da wannan kungiyar ce shekaru 6 da suka gabata da niyyar taimakawa wa matasan Afirka ta fannin kasuwanci, kare hakkin bil adama da kuma taka rawa a harkokin rayuwar yau da kullun.
Yau nahiyar Afirka ita ce keda dinbin albarkatu da damar ci gaba a kan harkokin rayuwa daban-daban.
Shugaba Obamna ya shaidawa taron mahalarta wannan taron cewa ya ziyarci yankin nahiyar ta Africa har sau hudu fiye da duk wani shugaban Amurka.
Yace wasu daga cikin abubuwan da yayi ko sun hada da ganin ya samar shine kara dankon zumunta tsakanin Amurka da Africa ta hanyar bunkasa cinikayya, samar da mulki nigari,kare hakkinbil adama, tsaro tare da ganin, jamaa sun wadata da abinci.
Yace ba sunyi haka bane domin kawai suna son mutanen Africa ne kawai ba, a’a sai domin duniya ba zata iya shawo kan matsalar canjin yanayi, da kuma ayyukan taddanci ko kuma fadada yancin mata, da dai sauran matsalolin da al’ummar duniya ke huskanta.
ba.