Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afrika Za Suyi Rawar Gani A Wasannin Rio Olympics Kuwa?


Wasan Kwallon Kafa na 'Yan Mata
Wasan Kwallon Kafa na 'Yan Mata

A cikin jerin shirye-shirye da ake gudanarwa na fara wasani daban daban mai take "RIO" a kasar Brazil, a gobe idan Allah ya kaimu. Wannan shine karo na farko da za’a gabatar da wasannin Olympics a kasar ta Brazil. Zakarun ‘yan wasan kwallon kafa na mata ‘yan kasar Sweden sun gwabza da ‘yan matan kasar Afrika ta kudu.

‘Yan wasan na kasar Afrika ta kudu sun sha kashi, da ci 1 da babu, ‘yar wasa Nilla Fischer, ta kasar Sweden ta fara da saka kwallo daya, cikin mintoci saba’in da biyar da fara wasan, haka wannan shine zai kasance karo na uku da ta halarci wasan zakaru na Olympics.

Su kuwa ‘yan mata ‘yan kasar Brazil zasu kara da ‘yan matan kasar China, ana dai sa ran wasanin da aka buga jiya da yau Alhamis, sune na share fage don fuskantar wasan gadan gdan a ranar Juma’a idan Allah ya kai rai. Za’a kunna wutar wasan a filin kwallo na Maracan, fillin da aka buga wasan cin kofin duniya shekaru biyu da suka wuce.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG