Jiya Laraba, shugaban Amurka Donald Trump yayi dana sani nada Session da yayi a zaman baban lauyan gwamnati ko kuma atoni janaral, domin Session bai yi wata wata ba ya tsame kansa daga binciken alakar dake akwai tsakanin yakin neman zaben shugaba Trump da kasar Rasha, sabili da ganawar da yayi da jakadan Rasha anan Amurka.
Shugaban Trump ya sha nuna takaicin yada Session ya tsame kansa daga binciken, ya bar shi ba tare da wanda zai yi masa biyaya ya kare shi ba. A saboda wannan takaicin, aka yi ta yayata jita jitan cewa kila shugaban na Amurka ya kori Session daga wannan mukami ya maye gurbin sa da wani.
To amma manyan yan jam’iyar Republican sun yiwa shugaban kashedi cewa kada ya kuskura ya kori Session suna tsoron cewa yin haka na iya zama dalilin tsige shugaban daga kan ragamar mulki.