Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Zai Yi Taron Share Fage Da Shugaban Japan Kafin Ya Gana Da Na Koriya ta Arewa


Firayim Ministan Japan Shinzo Abe da Shugaban Amurka Donald Trump
Firayim Ministan Japan Shinzo Abe da Shugaban Amurka Donald Trump

A cewar jami'an kasar Japan shugabansu zai gana da shugaban Amurka kafin taron koli tsakanin Shugaba Trump da Shugaba Kin Jong Un na Koriya ta Arewa da aka shirya za'a yi watan gobe a Singapore

Shugaban Amurka Donald Trump, da Firai Ministan Japan, Shinzo Abe, za su yi wata ganawa kafin babban taron da aka tsara za a yi tsakanin Trump da shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong Un, a cewar jami’an kasar ta Japan.

Shugaba Trump ya tattauna da Abe a jiya Litinin, yayin da jami’an Amurka suka je Korea ta Arewa da Singapore, domin tsara yadda tattaunawar za ta gudana.

Sai dai Fadar gwamnati ta White House ba ta amsa tambayoyin da Muryar Amurka ta yi mata ba, kan ganawar ta Trump da Abe.

Kusan Amurkawa dubu 34 suka mutu a yankin Korea, sanadiyar ta-da jijiyar wuyar da aka kwashe shekaru uku ana yi a yankin.

A shekarar alif-dari-tara-da-hamsin-da-uku ne hankula suka kwanta a yankin, sanadiyar wani shirin tsagaita wuta da aka cimma, amma ba tare da an rattaba hannu akan wata yarjejeniyar zaman lafiya ba.

Trump da Abe dai za su halarci wani taron koli na tattalin arziki da za a yi na kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wanda za a yi Canada.

Jami’an Amurka da na Korea ta Arewa sun hadu a yankin Korea, wanda baya dauke da sojoji a ranar Litinin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG