Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Fara Sukar Jam'iyyar Democrats Da Kakkausan Lafazi Domin Zabe Mai Zuwa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Zaben 'yan majalisun Amurka dake zuwa a watan Nuwamba ya fara tsoratar da Shugaba Trump domin jam'iyyar Domokrats na kan gaba abun da ya sa ya soma suka da kakkausar lafazi tare da tsorata 'yan kasar

A cikin watan Nuwamba mai zuwa ne masu jefa kuri’a anan Amurka zasu jefa kuri’a na tsakiyar lokaci ko wa’adi na wakilan Majalisar dokoki, wanda yanzu haka dai majilisun dokoki biyu na da rinjayen jamiyyar Republican, sai ga bisa dukkan alamu malisar Dattijai tana cikin rudu da damuwa.

Domin ko sakamakon wannan zaben na iya kawo wa shugaba Donald Trump nakasu, kuma yanzu haka shugaban ya fara lura da hakan.

Ba mamaki wannan yasa a wajen wani gangami makamancin na yakin neman zaben da shugaban ya fara a Washington da Michighan, Trump ya fara magana da kakkausar lafazi akan jamiyyar adawar sa ta Democrat, yana cewa muddin akasa wa Democrat kuri’a a watan nuwamba to ku kwana da sanin cewa bakin iyakar kasar ku yana bude wagaga, sai kuma masu aikata laifuffuka.

Kamar yadda wani shafin yanan gizo mai suna Real Clear, ke cewa jamiyyar Democrat tana da alamun galaba akan Republican da maki 7

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG