Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Larabar Amurkawa Suka San Trump Ya Biya Matar Da Ta Zargeshi Da Yin Lalata Da Ita - Sanders


Sarah Sanders sakatariyar watsa labaran Fadar White House
Sarah Sanders sakatariyar watsa labaran Fadar White House

Ranar Larabar shugaban Amurka ya amince ya biya matar da ta zargeshi da yin lalata da ita ta hannun lauyansa

Sakatariyar yada labarai ta Fadar White House ta fada jiya Alhamis cewa sai a ranar Laraba da dare ne ita da wasu Amurkawa suka san cewa shugaban Amurka Donald Trump ya biya lauyan sa kudin da lauyan ya biya ‘yar wasan kwaikwayon tsiraicin nan kafin lokacin zaben sa a shekarar 2016.

Da aka matsa wa Hukabee Sanders lamba, akan cewa kila ta shara karya ne ko kuma an barta cikin duhu game da wannan batun, a lokacin da ta shaidawa manema labarai cewa shugaba Trump bai san da batun biyan wannan matar wasu kudade ba.

‘’Tace na bada ainihin labarin da na sani ne game da wannan lamari a wannan lokacin”

Sai dai a farkon jiya alhamis ne Trump da kansa ya tabbatar da wannan batun a shafin sa na Twiter game da abinda dayadaga cikn lauyoyin sa ya fada.

Rudy Giuliani ya fada wa gidan talabijin na Fox a cikn shirin yamma cewa, ba shakka shugaba Donald Trump ya mayar wa Lauya Micheal Cohen da kudin sa da ya baiwa Stormy Daniels.

Wannan bayanin dai ya sabawa bayanin farko da shugaba Trump ya bayar game da wannan al’amari.

Sai dai kuma wata da ya wuce lokacin suna cikin jirgin shugaban kasar Amurka da ake kira Air Force One, da wani dan jarida ya tambayi shugaba Trump ko yana sane da wannan batun biyan kudin da lauyan sa yayi wa ita wannan matar Sormy Daniel? Sai Trump yace bai san dalilin dayasa lauyan say a biya ta wadannan kudaden ba.

Ita dai wannan mai wasan fitowa a cikin fina-finan batsa wadda sunan ta na gaskiya shine Stephanie Gregory Cliford tacesun taba kwana tare da shugaba Donald Trump a cikin shekarar 2006 a wani Hotel dake Nevada.

To sai dai lokacin da wanan batu ya kunno kai nan da nan Shugaba Trump shi da Lauyan sa suka ce ba wata dangantaka ta saduwa da wannan matar, kuma ba a bata ko anini ba ciki kudin kanfe din Trump ba.

Trump dai ya dage akan wannan batu da aka cimma matsaya da ita Daniels ba wani sabon abu bane a cikin mutane da suka yi fice da kuma masu hannuda shuni, sai dai yace amma kuma za a yi anfani da wannan domin neman kudin fansa na bata suna, domin ko tamkar ta karya ka’idar yarjejeniyar daaka cimmawa da ita akan wannan lamari saboda hirar da tayi da manema labarai.

To amma ita wannan mace tace yarjejeniyar bata da amfani domin shugaba Trump bai sanya hannu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG