Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Sake Sukar Binciken Zargin Kutsen Da Aka Yiwa Rasha Kan Zaben 2016


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Da kakkausan lafazi Shugaban Amurka ya sake sukar binciken zargin cewa Rasha ta yiwa zaben kasar na 2016 katsalandan inda ya hakikance akwai wata manufa daban musamman yadda jaridar New York Times ta samu tambayoyin da ake son yi masa

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake wani suka da kakkasau lafazi a jiya talata game da binciken aikata ba dai-dai ba game da alakar dake tsakanin yakin neman zaben sa da kasar Rasha da kuma take taken sa a fadar White House.

Shugaban na Amurka ya nuna shakkun sa akan binciken da Robert Mueller yayi, domin ko ya bayyana shi a matsayin abin kunya, domin akwai tambayoyi masu tarin yawa da masu bincike suke son su yiwa shugaba Trump. Amma kuma wadannan tambayoyin an tsegunta su ga Jaridar New York Times, akan haka yake tababan cewa da wahala a iya kawo wa wannan binciken cikas, idan kamar yadda yace babu wani hadin baki da kasar Rasha domin samun nasara a zaben nasa.

Rahoton na Jaridar New York Times yace tawagar ta Mueller tana son ta binciki tunanen da Trump keyi game da abinda ya faru lokacin yakin neman zaben nasa, a kusan watanni ukku kafin zaben sa da kuma lokacin da ya karbi ragamar mulki a cikin watan janairun shekarar 2017, da kuma watanni 15 da ya kwashe a kan karagar mulki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG