A jiya Alhamis, Shugaban na Amurka ya ce lura da harin da aka kai a Brussels, ba wai kawai za a yi Magana ne akan batun makamashin nukiliya, har da ma daukan matakan da za a dauka wajen kawar da ‘yan ta’adda.
Wannan na taron koli, wanda zai kasance nan a hudu na kuma karshe ga shugaba Obama wanda ke shirin kammala wa’adinsa, na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar mayakan IS ka iya yin amfani da fasahar ta nukiliya da kuma kasar Korea ta Arewa da ke kokarin bunkasa wannna fannin.
Mafi yawan shugabannin duni8ya da suka halarci wata liyafa a Fadar White a jiya Alhamis, sun fito ne daga kasashen da ke fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’adda.
A kuma wata liyafa da aka yi ta daban ofishin harkokin wajen Amurka, Sakatare John Kerry, ya ce a ‘yan lokutan bayannan, an dan yi sakaci game da batun kare yaduwar makamin na nukiliya.