Obama ya gana da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye da Firayim Ministan kasar Japan Shinzo Abe, a kadaice wajen taron kolin, domin tattauna barazanar da Koriya ta Arewa ke yi bayan gwajin makaman nukiliya a watan Janairu da kuma makami mai linzami mai cin dogon zango a watan Fabrairu.
Obama yace, “bakinmu ya zo daya a yunkurinmu na dakilewa da kuma kare kai daga takalar Koriya ta Arewa.
Batun Koriya ta Arewa ne ya kuma dauke hankali lokacin da Shugaba Obama ya zauna da takwaransa na kasar China Xi Jinping daga baya.
Washington, tana daukar Beijing a matsayin abokiyar kawance,wadda take da muhimmanci a aiwatar da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya kan Koriya ta Arewa sabili da bunkasa makamai da take yi.
A wata ganawa bayan nan, shugaban Obama ya yabawa takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande sabili da hada kan al’ummar kasashen turai a yaki da ta’addanci. Obama zai kuma gana da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
A wani rahoton bayyana ra’ayi na jaridar Washington Post, Obama yace shugabannin kasashen duniya zasu dauki mataki kan barazabar da kungiyoin ta’addanci kamar ISIS suke yi.