A yanzu haka, ana can ana ci gaba da aikin ceto mutanen da fallayen kankare suka fado suka rutsa da su a karkashin gadar. Haka kuma an tura kungiyoyi daga hukumar bada agajin gaggawa ta Indiya da ake kira NRDF a takaice da jami’an soja wurin don bada agaji. Kafin isarsu wurin dai, mazauna garin da ‘yan kwana-kwana sun yi ta amfani da hannayensu a kokarin tono mutanen da gadar ta afka a kansu.
Darakta janar din hukumar ta NRDF O.P Singh ya ce, su na samun labarin rushewar gadar, cikin gaggawa suka kira kwamishinan hukumar bada agaji na jihar, kuma nan take suka tura kungiyoyin bada agaji guda biyu zuwa wurin. Yace an ma ci sa’a wadannan kungiyoyin agaji suna wata unguwa cikin birnin na Kolkata a lokacin da wannan hatsarin ya abku.
Shaidun gani da ido sun ce akwai mutane da motoci, ciki har da wata bas dauke da fasinjoji fiye da 100 da motocin Tasi da dama karkashin gadar a lokacin da ta rufta. Masu aikin ginin gadar, da ke aiki tukuru don kammala ginin, sun kafa sansaninsu kusa da gadar inda suke barchi da kuma dafa abinci.