Hamshakin attajirin nan dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin tutar jam’iyyar Republican dake kan gaba Donald Trump ya sake samun kansa cikin wata sabuwar matsala jiya alhamis, bayanda ya yi kira da a hukumta matan da suka zubar da ciki muddin an haramta yin haka a kasar, ko da yake ‘yan sa’oi bayan ya fadi haka ya sake maganarsa.
A wata hira da tashar CNN, game da kalaman na Trump, kakakinsa, Katrina Pierson tace, babu shakka wannan barin baki ne, tace dama Trump yana da gagarumin goyon bayan ‘yancin mata na neman taimakon ma’aikatan lafiya, yanzu kuma yana goyon bayan haramta zubar da ciki da sharuda, zai kuma goyi bayan hukumta likitocin da suka zubarwa mata da ciki ba matan ba, idan kotun koli ta soke hukumcin da aka yanke shekaru 43 da suka shige da ya bada ‘yancin zubar da ciki.
Abokan hamayyar Trump duka biyu, gwamnan jihar Ohio John Kasich da dan majalisar dattijai daga jihar Texas Ted Cruz duka suna adawa da ‘yancin zubar da ciki.
Binciken ra’ayoyin jama’a ya nuna kashi saba’in cikin dari na mata basu goyon bayan Trump.
Kalaman na Trump sun zo kwana daya bayanda ya kare manajan yakin neman zabensa Corey Lewandowski wanda ake tuhuma da murde hannun wata mace ‘yar jarida da take daukar rahoton yankin neman zabensa a jihar Florida cikin watan Maris.