Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam ya kashe jami'an 'yansanda a Turkiya


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

A Turkiya, wani harin bom da aka kai a wata mota ya kashe jami’an ‘yansanda shida, ya kuma jikkata a kalla mutane 23 jiya Alhamis, a birnin Diyarbakir dake kudu maso gabashin kasar, inda galibin mazauna wurin Kurdawa ne.

Bisa ga kafofin sadarwar kasar Turkiya, bom din ya tarwatse ne a daidai lokacin da wata mota dauke da jami’an ‘yansanda na musamman suke wucewa a babbar tashar motocin safa ta birnin.

Nan da nan, babu kungiyar da ta dauki alhakin harin. Bijirarrar Kungiyar Kurdistan Worker Party (PKK) ta dauki alhakin wadansu hare haren bom biyu da aka kai farkon shekarar nan a Ankara babban birnin kasar.

Mutane ishirin da bakwai ne suka mutu galibi sojoji a ranar goma sha bakwai ga watan Fabrairu lokacin da mayakan PKK suka kai hari kan motar safa da suke ciki. Ranar goma sha uku ga watan Maris kuma, wata fashewar nakiya da ‘yan tawayen Kurdawan suka dauki alhaki ya kashe mutane 37 da suka hada da ‘yan harin kunar bakin waken biyu.

Har wayau, harin kunar bakin wake da aka kai a Istanbul ranar goma sha tara ga watan Maris ya kashe mutane biyar yayinda a kalla 36 suka jikkata.

XS
SM
MD
LG