Shugaba Muhammadu Buhari Ya Gana Da Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Buhari Tare Da Shugaba Trump Yau A Fadar White House

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da takwaransa na Amurka Donald J. Trump, inda suka tattauna akan abubuwa da suka shafi tsaro, tattalin arzikin kasa kana da harkar noma.

A tattaunawar, sun yi magana akan irin gudunmawa da kasar ta Amurka ke ba kasar Najeriya, inda ya bayyana cewar kasar Amurka taba Najeriya gudunmawar kudade ko a shekarar da ta gabata, da suka kai dallar Amurka billiyan daya, acewar shugaban Amurka.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewar Amurka taba da makudan kudade da suka kai kimanin rabin billiyan ta hannun majalisar dinkin duniya, wanda akayi amfani da su wajen kara inganta tsaro a kasar.

Kana gwamnatin Amurka a shirye take don ganin ta taimaka ma Najeriya da makamai da horas da sojojin Najeriya don yaki da ta’addanci. Shugaba Buhari ya yabama gwamnatin Amurka dangane da irin gudunmawar da kasar ta Amurka ke ba Najeriya ta bangarori daban daban.

A lokacin da ‘yan jarida su kayi ma shgaba Buhari tambaya dangane da kalaman batanci da shugaban Amurka yayi akan kasashe masu tasowa, shugaba Buhari, yaki cewa komai dangane da hakan, sai yace “bamu tattauna da shugaba Trump akan wannan maganar ba, domin kuwa yana tunanin cewar wannan maganar kagen ‘yan jarida ne”