Bazoum Ya Maka Sojojin Juyin Mulki A Kotun ECOWAS

Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum

Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya shigar da sojojin da suka yi juyin mulki kara a kotun ECOWAS/CEDEAO sakamakon zargin tsare shi da iyalinsa ba akan ka’ida ba.

Bazoum ya bukaci kotun da ta kwato masa hakkinsa daga wadanda suka toye masa ‘yancinsa na yawutawa da dai sauran ‘yanci masu nasaba da hakkokin bil adama.

Tun a ranar 26 ga watan Yuli ne sojojin fadar shugaban kasa suka tsare shugaba Bazoum da iyalinsa a fadarsa kafin daga bisani su bada sanarwar kifar da shi daga karagar mulki abinda kungiyar ECOWAS ta ce da sake.

Ta hanyar lauyansa Maitre Mohamed Seydou Diagne mai ofishin a birnin Dakar na kasar Senegal ne shugaba Mohamed Bazoum ya maka hukumomin Nijer a kotun CEDEAO da yake zargi da toye masa wasu jerin hakkokinsa. Wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da sahihahincin Kofin tarkardun wannan kara da suka karade kafafen sada zumunta.

Hamabaren shugaban ya bukaci kotun ta ECOWAS ta yi la’akari da yadda aka toye masu ‘yancin kai da kawo da shi da maidakinsa Hadiza Mabrouk Bazoum da dansa Salem Bazoum.

A karkashin wadanan tuhume-tuhume Mohamed Bazoum ta hanyar lauyansa ya bukaci kotun ta bada umurnin gaggauta sakinsu daga inda ake tsare da su sannan lauyan ya bayyana fatan ganin kotun ta fahimci yadda aka toye wa mutunen da yake karewa ‘yancin gudanar da harakokin siyasa.

A bisa la’akkari da dukkan wadanan batutuwa, lauya maître Mohamed Seydou Diagne ya yi kiran kotun CEDEAO ta dauki matakin tilasta wa mutunen da ya kira mai kiran kansa shuagban kasa ko gwamnatin Nijar su yi biyayya ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.

Wani na hannun daman hambararen shugaban Dr. Haboubacar Manzo ya yaba da wannan mataki da ya kira na halin dattako.

Kotun ta CEDEAO ta yi na’am da wannan kara koda yake ba ta tsayar da ranar sauararen bangaorin ba amma kuma ta aike wa hukumar shara’ar Nijer wato AJE takarda don sanar da ita karar da ke gabanta.

Kawo yanzu majalisar CNSP da gwamnatin rikon kwaryar Nijar ba su bayyana matsayinsu ba akan wannan lamari.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Bazoum Ya Maka Sojojin Juyin Mulki A Kotun ECOWAS