Serena Williams Ta Kai Zagaye Na 2 Na Gasar Roland Garros

  • Murtala Sanyinna

Serena Williams

‘Yar kasar Amurka Serena Williams ta soma fafutukar lashe kofin babbar gasar Tennis na 24 a tarihi.

Serena Williams ta doke takwarar ta ‘yar kasar Amurka Kristie Ahn, a wasan su na farko ta bude gasar French Open ta bana.

Williams mai shekaru 39 da ke matsayin mace ta 6 a duniyar Tennis, ta doke takwarar tata ne da turmi 2 a jere a zagayen na farko na gasar.

Wannan ya ba ta damar tsallakewa zuwa zagayen na 2, inda za ta fafata da ‘yar kasar Bulgaria Tsvetana Pironkova.

Pironkova, mai shekaru 33, ta sami shiga gasar ta Roland Garros ne sakamakon gayyata ta musamman da ta samu daga masu shirya gasar, biyo bayan kwazon da ta yi a gasar US Open da aka kammala kwanan nan, inda Williams din ta doke ta a zagayen quarter-finals na gasar.