A ranar talatar da ta wuce fitacciyar ‘yar wasan kwallon hannun nan Serena Williams, ta bayyana cewa bata yi niyyar bayyana ma duniya, juna biyunta ba, mai tsawon sati 20, sai dai ta kuskure ta saka hoton a shafin sadar da takaittacen zumunci “Ssnapchat” a turance.
Williams da ke sanye da dorowar rigar shakatawa, a hoton da tayi saurin goge shi a shafinta, amma daga baya ta gazgata labarin daga bakin mai magana da yawunta, bayan dogon takaddama akan hakan.
Ta bayyanar da hakan ne a wani taron karama juna sani na TED a kasar Vancouver, cewar hoton, ta yi shi ne kawai saboda ajiyarta.
Ina da wannan halin na duba kaina da daukar hotuna, duk sati don ganin cigaban da juna biyun nawa yake samu, ‘yar shekara 35, din ta bayyana wa dan jaridar nan Gayle King.
Nakan adana ma kaina hotunan ne, kuma ina matukar kokari wajen yin hakan kafin a samu wannan kuskuren.
Ta fadi cewa ta gane tana da juna biyun ne, kwana 2 kafin a bude gasar wasanin da aka fafata a kasar Australia, a watan Janairu. Wanda taje da niyyar lashe kambun a zagaye na 23.
Williams wadda zata dauki hutun haihuwa har zuwa karshen zangon shekarar 2017, tace babu wani canji a tsarin ta na dawowa wani zangon a matsayin uwa.
Tace zaman ta na uwa wani sabon abu ne a rayuwarta, tana fatan abunda ta haifa wata rana ya shiga cikin rumfa yana ihu yana kara mata karfin gwiwa.
Facebook Forum