Shahararriyar ‘yar wasan kwallon Tanis Serena Williams, ta tabbatar da cewar tana bukatar sake lashe kambun ‘Grand Slam’ matashiyar Sarena, ta lashe kambun sau 23 a tsawon rayuwarta ta wasan Tanis.
Serena, nahutu tun bayan haihuwar da tayi a watan Satumba, inda ta samu diya mace da aka radamata suna Olymkpia. Ta bayyanar da cewar tun bayan haihuwar ta taji jikin ta yayi sanyi, kasancewar yanzu tana shayarwa.
Ta shaida cewar a irin mataki da ta samu kanta a rayuwa, bata bukatar wani kudi ko kuma sake daukar wani kambu, tana ganin babu abun farinciki a rayuwa da ya wuce a ce mutun ya haihu.
Amma yanzu tun bayan haihuwar Olympia, taji karfinta da kuzarinta ya dawo matuka, don haka yanzu a shirye take ta sake komawa fagen daga don ganin ta sake lashe kambu.
Facebook Forum