Maria Sharapova, shahararriyar ‘yar wasan “Long Tennis” ce a duniya ‘yar kasar Rasha. A yau dai kungiyar ‘yan wasan Tennis ta nan kasar Amurka, ta fitar da wata sanarwar cewar, wannan ‘yar wasan baza ta samu damar buga wasan zakaru na duniya ba, da za’a buga kwanakin nan.
Maria dai wannan shine karo na biyu da take kauce ma shiga wannan gasar, duk dai da cewar an bayyanar da cewar, baza ta samu buga wasan ba ne a dalilin rauni da ta samu a kafarta. Ta rubuta a shafinta na Facebook cewar. “Zuwa ga dinbin masoya na, zan dawo lokacin wasan kasar Asia, nan da wasu makwanni, ina kuma fatan gama wanna shekarar cikin koshin lafiya”
Wasan dai da ta buga na karshe, shine wasan da suka yi da ita da wannan shaharariyar mai wasan ta duniya wato Serena Williams, yar kasar Amurka. Wasu ma na ganin kamar cewar Maria na gudun shiga wannan gasar ne, domin tana tsoron karon battar ta da ‘yar wanan kasar ta Amurka mai shekaru 32. Amma ta musanta wannan kalamin.
Facebook Forum