Serena Williams mai kare kambinta na wasan kwallon Tennis a gasar kasa da kasa ta Olympic, jiya Lahadi ta daure duk da tsananin iska, sai da ta yi nasarar kaiwa zagaye na biyu, bayan da ta doke Daria Gavrilova ta Australia da ci 6-4; da kuma ci 6-2, yayin da ake ta sukar jami'an wasannin da gudanar da shi cikin yanayin da bai dace ba.
Iskar, wadda ke gudun kilomita 25 cikin sa'a guda ta sa an dage wasan na jiya Lahadi da minti 90, yayin da iskar ke ta bararraka dandalin wasan Barra da ke Rio de Janeiro.
Facebook Forum