A wani sako da ta aikowa Muryar Amurka kungiya SERAP ta nemi gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye sunayen wasu ‘yan tsirarun PDP da ministan labaran kasar Alhaji Lai Mohammed ke cewa sune suka handame dukiyar kasa.
Maimakon haka, kungiyar ta nemi gwamnatin ta fito da cikakken sunayen duk wadanda ke da hannu wajen wawure dukiyar ‘yan Najeriya.
Da yake mayar da martani kan batun cewa jam’iyyar PDP ta dawo da kudaden da ake zargin ta sata, tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya yi zargin cewa kudin da aka sata shi ne aka yi amfani da su wajen kamfen din shugaba Buhari a shekarar 2015.
A cewar Sule Lamido, wasu ‘yan PDP ne suka dauki kudaden da suka sata suka yi amfani da su wajen zaben shugaba Mohammadu Buhari, wanda hakan ke nuna cewa "barayin ‘yan PDP" ne suka kafa wannan gwamnatin.
Wani na hannun damar shugaba Buhari kuma tsohon gwamnan jihar Yobe, Alhaji Aliyu Saleh Bagare, ya ce bai yarda da wanan kalamai da Sule Lamido ya yi ba.
Bagare ya jaddada cewa ‘yan jam’iyyar PDP ba abin da suka yi a lokacinsu sai wawure kudaden kasar.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5