Gwamnatin Zamfara dai ta dauki wannan mataki ne domin kawo karshen kai hare-hare da kashe-kashen jama’a, da 'yan bindiga ke yi.
Amma 'yan bindigar, wadanda aka sha zaman sulhu da su, sun ce wannan ba ita ce mafita ba.
A martanin da ya mayar, gungun ‘yan bindigar marigayi Buharin Daji wanda ya dauki alhakin harin baya-bayan nan a garin Bawar Daji da ke karamar hukumar Anka, ya ce wannan mataki ba zai samar da zaman lafiya ba a jihar.
Wani da ya kira kansa Mohammad Bello, a matsayin wanda ya gaji Buharin Daji a shugabancin gungun ‘yan bidigar, ya shaidawa Muryar Amurka ta wayar talho cewa harin da suka kai garin Bawar Daji na ramuwar gayya ne, bayan da aka kama yaransu da matansu.
Duk da haka ‘yan bindigar sun ce a shirye suke su rungumi duk wani shiri na sulhu da sasantawa amma bisa sharadin sai an daina kama ‘yan uwansu tare da korarsu daga gari.
Amma da Muryar Amurka ta tuntubi gwamnan jihar Abdul’aziz Yaro, ya ce su kam a yanzu sun cimma matsayar sanya kafar wando daya ne kawai da maharan, saboda gazawar matakin sulhu da aka dauka a can baya.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna:
Facebook Forum